✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ɗaure matashi shekara 8 kan satar wayar taransufoma

Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin shekara takwas kan satar babba wayar taransufoma

Kotu ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 26 daurina shekara takwas a gidan yari bisa laifin satar wayar tiransufoma mai nauyin kilogiram 37, wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan ɗaya a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Damaturu a Jihar Yobe.

Lauyan masu shigar da kara na hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), Barista Jidda Abdulqadir, ya shaida wa Mai Shari’a Fadima Murtala Aminu na Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu, cewa wanda ake zargin ya cire tare da satar wayar taransfoma.

Masu gabatar da kara sun gamsar da kotun da ingantattun shaidu da suka baje koli daga sashen leken asiri da bincike na rundunar.

Wanda aka yanke wa hukuncin, tare da wani (da har yanzu ba a kama) ba, sun lalata taransfoma a makarantar a ranar 8 ga Satumba, 2024, kuma a washegari aka kama shi Nasiru Lawan a wajen sayar da wayar tiransufoma.

A yayin yanke hukuncin, alƙalin ta yi Allah wadai tare da nuna rashin jin daɗinta kan ayyukan barayi a jihar, tana mai bayyana su a matsayin masu zagon ƙasa ga tattalin arziki da zamantakewa.

Ta bukaci hukumomin tsaro da su ƙarfafa haɗin gwiwar a tsakaninsu domin daƙile munanan ayyukan da suke yi.