Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin New York na Amurka don nuna goyonsu bayansu ga Falasdinawa kan gwabzawar da Isra’ila take yi da kungiyar Hamas.
Mutanen dai na kira ne ga Isra’ila da ta kawo karshen mamayar da take yi wa Falasdinawa sannan a ’yanto su daga Yahudawa.
Sun mamaye tituna da manyan hanyoyi da dama a cikin birnin da yake zama tamkar wata hedkwatar ’yan kasashe da mabiya addinai daban-daban na duniya.
Masu zanga-zangar, wadanda galibinsu matasa ne dai sun rika daddaga tutar kasar Falasdinu sannan suna zargin Isra’ila da aikata kisan kiyashi, inda suka roki Amurka ta janye goyon bayan da take ba su.
Tun a ranar Asabar din da ta gabata ce dai Hamas ta kaddamar da hare-hare inda suka harba dubban rokoki zuwa cikin Isra’ila, inda suka kashe sama da mutum 1,300, galibinsu fararen hula.
Sai dai Isra’ila ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu sarrafa kansu a cikin birnin Gaza, wanda ya yi sanadiyyar kisan Falasdinawa akalla 1,900, galibinsu fararen hula, ciki har da kananan yara sama da 600.
Kawo yanzu dai ana ci gaba da gudanar da zanga-zanga a sassan duniya daban-daban domin nuna goyon bayansu ga ko dai Isra’ila ko kuma Falasdinawa.