✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El Molo: Ƙabila mai mutum 99 kacal a duniya

’Ya’yan wannan kabila ta El Molo na daga cikin kabilun kasar 70, babar sana’arsu farauta da kamun kifi.

A bisa al’ada duk duniya, duk inda aka haihu ana murnar samun wannan karuwa, amma ba haka abin yake ba a kabilar El Molo da ke kasar Kenya.

Domin a wannan kabila a duk lokacin da aka haihu dole a mutu don kada yawan mutanen wannan kabilar ya wuce 99.

’Ya’yan wannan kabila ta El Molo na daga cikin kabilun kasar 70, babar sana’arsu farauta da kamun kifi kasancewar suna zaune ne a bakin Tafkin Turkana a Kudancin Loiyongalani da ke Kudancin kasar.

Rahotannin sun ce ’ya’yan kabilar suna zaune ne a wani kauye gaban dayansu kwansu da kwarkwatarsu maza da mata manya da yara da kuma tsofaffi su 99.

Idan aka samu karin mutum daya, dole daya daga cikinsu ya bar duniya ko da shiri ko babu.

A bisa al’adar wannan kabila da zarar an haifi jariri za a sanar da manya inda cikin wadanda suka tsufa za a fitar da mutum daya wanda a dole ya bar duniya mace ce ko namiji.

Wanda kuwa waki’ar ta fada kansa ba ja, sai ya saduda ya shirya ya tafi Lahira.

Duk wanda hakan ta faru gare shi yakan karbi kaddara tare da alfaharin cewa hakan shi ne daidai kuma abin alfahari na bin tafarkin iyaye da kakanni da suka gadar musu.

A cewar ’ya’yan wannan kabila suna samun wahayi ne ko shiriya daga yanayi na taurari da ke shiryar da su kan wanda ya kamata ya mutu a cikinsu da zarar an haihu a kabilar don kada su cika 100 balantana su haura haka.

Sai dai da zarar an yi haihuwa za ka gan su cikin rashin natsuwa ko walwala, har zai an fitar da wanda zai mutu ko da mai haihuwar ce kuwa.

Sai dai babu bayanin yaya wanda aka zaba yake mutuwa, kashe shi ake yi ko haka kawai zai mutu?

Kafar labarai ta Afrimad ta Ingilishi da ta gano wannan kabilar ta ruwaito cewa an taba samun wani lokaci da yawan ’yan kabilar ya kai 100 amma na dan wani lokaci ne a cikin kwana da yini daya a inda nan da nan manya suka taru suka warware wannan abin da suka kira ‘babban sabo.’

Kabilar El Molo maguzawa ne da suka ayyana WAAK/WAHK a matsayin abin bautarsu.

Kuma sun dogara ne da Tafkin Turkana domin gudanar da rayuwarsu kasancewarsu masunta kuma manoma.

An bayyana yawaitar fari a wasu lokuta da karancin gonaki da karancin ruwan sha suna daga cikin dalilan da suke hana karuwar kabilar.

Sai dai ’ya’yan na iya karuwa idan suka yi aure da wasu kabilun kamar kabilun Rendile, Turkana da Samburu.

Wanda hakan ke nuna mutum ya tashi daga tsantsar dan kabilar El Molo.