Al’ummar Kauyen Gwarimpa da ke yankin Birnin Tarayya Abuja sun samu kansu a cikin zullumi bayan rigima ta faru a tsakanin Hausawa da ’yan kabilar Gbagyi, wadda ta yi sanadiyyar rasa rai da kuma dukiya.
Rigimar wadda ta faro a ranar Asabar da ta gabata, ta ci gaba zuwa ranar Litinin, inda hukumomi suka tabbatar da rasuwar mutum guda, sai wadanda suka samu raunuka da kuma asarar dukiya da ta hada da lalata baburan Keke-NAPEP da wuraren sana’a ko kasuwanci na Hausawa, sai kuma motoci da yawancinsu na ’yan kabilar Ibo ne da ke tsaye a gaban shagunansu, mallakin ’yan kabilar Gbagyi.
- Mutanen Kaduna sun koka kan matsalar wutar lantarki
- An kashe hatsabibin dan ta’adda ya je garkuwa da dan kasuwa a Katsina
Rundunar ’Yan sandan Abuja ta bakin kakakinta, S.P Josephine Adeh ta tabbatar rasuwar mutum guda.
Bangarorin biyu da Aminiya ta zanta da su sun ba da tabbacin cewa rigimar ta faro ne da wasu masu harkar sayar da miyagun kwayoyi a yankin, wadanda Hausawa ne amma bayan sun gudu sai rigimar ta koma kan sauran Hausawa da ke sana’ar tukin Keke-NAPEP da kuma ’yan gwangwan, sai ’yan kasuwa da suke zaune a baca.
Wani malami mai suna Shu’aibu Tela ya ce lamarin bai rasa nasaba da jawabin bayan hudubar Sallar Idi da aka gabatar kan illar miyagun kwayoyi da kuma bukatar al’umma su ba da gudunmawa wajen yakar lamarin ba, kasancewar hukuma kadai ba za ta iya aikin ba.
Ya ce nan take hakimin garin, Alhaji Umar Bayero ya sha alwashin yakar lamarin ko da hukuma ba ta goya masu baya ba.
Unguwar Gwarimpa Village yanki ne na ’yan asalin Abuja da ke rike da sarautar gargajiya ta Dagaci da Hakimi, inda yake da al’ummar Hausawa masu yawa, sai kuma sauran kabilu kamar Ibo da ke gaba wajen mallakar shaguna a babban titin da ya ratsa unguwar, baya ga zama da wasunsu ke yi tare da iyalansu a yankin.
Wani mazaunin kauyen, Ahmad Auwal ya ce bayan Sallah da kwana guda, jami’an tsaro sun kai samame a kan wasu da ke harkar sayar da kwaya, amma sai suka tsere cikin unguwa.
“Sun auka wa wani dan kabilar Gbagi (Gwari) da bugu, inda suka gudu bayan sun gan shi yana yin waya, suna zargin shi ne ya gayyato ma’aikatan.
“Sun kwace wayar tare da tattakawa; Hakan ya fusata al’ummar Gbagyi (Gwarawa), inda suka kai farmaki kan masu harkar sayar da kwaya; suka sassari wasunsu da adda, suka bugi wasu da sanduna,” in ji shi.
Ya ce lamarin ya ci gaba a ranar Lahadin da ta gabata, bayan samun labarin wasu sun shigo unguwar bisa gayyatar masu harkar kwaya da nufin auka wa abokan rigimar tasu.
Sai dai Gwarawan ba su kai ga abokan fadan nasu ba, sai suka koma kan sauran al’ummar Hausawa, inda suka kashe wani matashi mai suna Isiyaka Ibrahim da ke zama a karkashin wani mai shagon kayan masarufi.
Ya ce matsahin ya je shan shayi ne da misalin karfe takwas na dare, sai matasan Gbagyi suka hau shi da duka da sara har sai da ya daina motsi.
Malam Abubakar Dahiru shi ne Shugaban Masu Tukin Keke-NAPEP a yankin, ya ce baya ga mutum guda da aka ba da tabbacin kashewa, akwai mambobinsu da dama da aka sassara, ciki har da wanda aka kai shi Asibitin Kasa sakamakon munin raunin da ya samu a kai.
Ya ce an lalata masu Keke-NAPEP guda 11, ciki har da wadanda suke tsaye da wadanda suke gareji wajen gyara.
Aminiya ta samu labarin cewa matasan Hausawa sun gudanar da zanga-zanga washegari Litinin, kan abubuwan da aka yi masu, na kisa da lalata dukiya, inda a yayin zanga-zangar aka fasa gilasan motoci da ke ajiye a gaban shaguna.
Suna zargin masu shagunan, wadanda yawanci ’yan kabilar Ibo ne da ke haya a wajen ’yan asalin yankin, da hada baki wajen far wa al’ummarsu da kuma kai wa dukiyarsu hari.
Aminiya ta zanta da wani mai suna Alhaji Abba Mai Kare, wanda ke sana’ar farauta da gadi da kuma gwangwan a yankin, wanda aka kashe wa karnuka 15 a yayin rigimar.
Ya ce matasa ’yan kabilar Gbagyi da adadinsu ya kai 20 sun je inda yake sana’a dauke da makamai, suka auka masa da sara. Sai dai ya ce Allah Ya taimaka ba su samu nasarar kashe shi ba.
“Sun ce da ni, tunda dai karfe ba ya shiga ta, to koda wuta sai sun kashe ni. A nan ne suka banka mini wuta a fuska, suka kuma rika buguna da dutse a fuska,” in ji shi.
Ya ce, “Sun kashe mini karnuka 14, suna sarawa sannan suna jefa su a wuta. Na 15 mai suna arne, bayan sun kula sara ba ta kama shi, sai suka daure shi da sarka, suka jefa shi cikin wutar.”
Alhaji Abba Mai Kare ya ce ya ji takaicin kashe masa wannan kare, kasancewar yana ji da shi kuma an saye shi kan Naira dubu 400 amma ya ki sayar da shi.
Ya ce wadanda suka auka masa sun yi masa rauni a fuska ta hanyar amfani da wuta da kuma dutse bayan sun kwantar da shi.
A zantawarsa da Aminiya, wani jagoran matasa a bangaren kabilar Gbagyi mai suna Idris Jeji, ya ce an lalata motocin ’yan hayarsu da suka kai 18.
Wakilinmu ya ga mota guda da aka lalata a kan babban titin da ya ratsa ta unguwar. Sai dai jagoran ya ce an kwashe yawancin motocin da aka lalata ne zuwa wuraren gyara.
Ya ce babu ko mutum guda da aka raunata ko aka kashe daga bangarensu.
Hakimin Gwarimpa, Alhaji Umar Bayero, kamar sauran wadanda aka zanta da su, ya danganta rigimar da matsalar harkar kwaya wadda ya ce ta zama babban kalubale ga rayuwar matasansu. Ya ce har a kofar asibitin yankin ake sayar da ita.
“Sun gawurta matuka, sannan sun shiga yi wa mutane kwace. Sannan duk yunkurin da muka yi na neman hukuma ta kawo mana dauki ya faskara saboda suna yin harkar ce cikin daurin gindi.
“Ba gaskiya ba ce a danganta wannan lamari da fadan kabilanci a tsakaninmu da abokan zamanmu Hausawa.
“Rigima ce a kan masu harkar miyagun kwayoyi da kuma abokan tafiyarsu ’yan bola, wadanda ba dama a ajiye abu a kofar gida, sai su sace su tafi da shi,” in ji hakimin.
Ya tabbatar da rasuwar mutum guda, sai wadanda suka tsira da raunuka, wadanda ya ce a iya saninsa suna raye har zuwa ranar Talatar da ta gabata, lokacin da wakilinmu yake zantawa da shi.