Fitacciyar ’yar jaridar nan, Toke Makinwa, ta ce ’yan fashi sun raba ta da wasu muhimman kayayyakinta a birnin London.
Makinwa, mai gabatar da shirye-shirye a rediyo da talabijin da ta sanar da fashin da aka yi mata ne ta shafinta na ‘Snapchat’.
- NAJERIYA A YAU: Matsayin Kuri’ar ’Yan Gudun Hijira A Zaben 2023
- Jami’ar Usmanu Danfodiyo za ta fara dashen koda
Ta ce, “Yanzu aka yi mini fashi a London, na ma rasa abin cewa. Ta yaya hakan za ta faru da ni?” inji ta.
Wasu ra’ayoin da aka bayyana a karkashin sakon da Toke Makinwa ta wallafa sun nuna London da Legas tamkar wa da kani ne inda ake fama da bata-gari, kuma akwai ’yan Najeriya mazauna birnin da daman gaske.
Idan za a iya tunawa, kwanan nan gwamnatin Najeriya ta shawarci ’yan aksar masu shirin zuwa Amurka da Birtaniya da wasu kasashen Turai da su yi hattara da barayi a can.