✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa sojojin da Boko Haram ta kora a Marte afuwa

Da farko an kwace kakin sojojin bayan Boko Haram ta kai hare-hare a sansaninsu

Runduna ta 7 ta Sojin Kasa ta Najeriya da ke Maiduguri ta amince da dawo da sojojin Bataliya da 153, Marte da mayakan Boko Haram suka kwace garin daga hannunsu.

Da farko Rundunar ta kwace kaki da da katin shaidar sojojin bayan da mahara suka kai wasu jerin hare-hare kan bataliyar da ke aiki daga sansanin tare da Birged ta 22.

Ana zargin mayakan sun samu galaba a wasu munanan hare-hare biyu tsakanin watannin Janairu da Fabrairun bana.

“An dawo da sojojin da abin ya shafa kuma an mayar musu da kakinsu da katin shaida.

“Za su kawo je Bataliya ta 212, 195 ko 159 gwargwadon inda sunayensu suka fito.

“Kodayake an maye gurbinsu a Marte tare da sojoji daga Babban Barikin Sojin da ke Jaji, Jihar Kaduna, da alama suna iya kasancewa a Borno duk da cewa suna can tun 2017,” inji majiyar.