✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa sojar da ta fada kogin soyayya da matashi mai yi wa kasa hidima a Kwara afuwa

Aminiya ta gano cewa an yi mata afuwar ne albarkacin bikin Kirsimeti.

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Lafatanar Janar Faruk Yahaya ya nemi a yi afuwa ga matashiyar sojar nan da ta fada kogin soyayya da wani matashi mai yi wa kasa hidima a sansanin ba matasan horo da ke Jihar Kwara.

Aminiya ta gano cewa an yi mata afuwar ne albarkacin bikin Kirsimeti, don ta je ta yi bukukuwa a gida tare da sauran iyalanta.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito daga wasu majiyoyi a rundunar cewa a ’yan kwanakin da suka gabata ne Babban Hafsan ya aike da bukatar neman yin afuwar ga shugabancin rundunar.

To sai dai Janar Yahaya ya tsaya kai da fata cewa dole a ja kunnenta kan ta kiyayi aikata duk wani abu da ya saba da tanade-tanade da dokokin rundunar, kamar yadda majiyar ta shaida.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya, wani faifan bidiyo ya karade gari, musamman a kafafen sada zumunta na zamani na wata macen soja tana karbar soyayyar wani matashi a sansanin ba da horo da ke Yikpata a Jihar Kwara.

A daya daga cikin faya-fayan bidiyon dai, an ga wani matashin da ba a kai ga tantance wane ne ba ya durkusa yana mika mata zoben soyayya, inda ita kuma ta karba cikin farin ciki, sauran matasa kuma suna yi musu shewa.

Daga bisani kuma, an hangi matashin a bayanta, yayin da ya ci gaba da sunbantarta, su kuma sauran matasa na daukarsu a bidiyo.

Sai dai daga bisani rahotanni sun ce Rundunar ta tsare sojar, lamarin da ya janyo cece-kuce da Allah wadai a kafafen sada zumunta na zamani.