An kama wani matashi ɗan shekaru 33 bisa zargin yin garkuwa da ’yar maƙwabcinsa mai shekaru 21 a ƙauyen Paikon Bassa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji a yankin Babban Birnin Tarayya.
Wani ɗan banga a yankin, Dangana Bala, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan samun ƙorafi daga iyayen matashiyar da ta ɓace na wasu makonni.
Ya ce iyayenta sun yi zargin mutumin, wanda suka ce ya daɗe yana soyayya da ita a ɓoye.
Ya ƙara da cewa da samu wannan bayanin, ’yan sintirin suka sanar da abokan aikinsu a ƙauyen Dafa da ke makwabta da su, kuma an gano matashiyar a ƙauyen Tukurwa da ke Ƙaramar Hukumar Kwali a ranar Lahadin da ta gabata.
- Wulaƙancin da ake mana a Kudu ya yi yawa —Hausawan Legas
- NAJERIYA A YAU: Yadda naira biliyan ɗaya ta salwanta a gobarar Kasuwar Jos
Ya ce ’yan sintirin sun gano cewa a ranar da ake shirye-shiryen Easter, mutumin ya fita da yarinyar a kan babur ya kai ta gidan abokinsa a ƙauyen.
“A gaskiya, iyayen yarinyar sun daɗe suna korafin cewa mutumin ya jima yana soyayya da ita a ɓoye. Har ma sun gargade ta da ta nisanci mutumin. A ranar Lahadi, ’yan sintirinmu da ke Dafa sun ga yarinyar da mutumin a kan babur, kuma nan take suka sanar da mu, muka je ƙauyen Tukurwa don kama shi a gidan abokinsa.”
Sun kuma ce tun farko mutumin ya musanta ɗauke yarinyar lokacin da iyayenta suka je wurinsa suna neman inda take.
Ya ce, “Daga baya mun samu labarin cewa ya fi shekara yana soyayya da ita da niyyar aure, amma iyayenta sun ƙi duk da cewa ya kashe kuɗi a kanta.”
Bala ya ce an miƙa mutumin da abokinsa da aka samu yarinyar a gidansa, ga jami’an tsaro a Kwali.
’Yan sanda a yankin sun tabbatar da faruwar lamarin.