✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa matashi yankan rago a cikin gidansu Filato

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi wa wani matsahi ɗan shekara 32 yankan rago a yankin Kampani da ke…

Wasu mahara sun yi wa wani matsahi ɗan shekara 32 yankan rago a yankin Kampani da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato.

Shugaban matasan yankin, Sapi’i Sambo, ya ce an yi wa matashin mai suna Usama Danladi, yankan rago ne a yayin da yake barci a ɗakinsa da dare.

Ya bayyana cewa mutanen gidan su Usama ne daga baya suka tsinci gawarsa cikin jini da wuyansa a yanke.

Yankin Kampani dai na yawan fama da matsalar ’yan fashin daji da sauran nau’i kan taddanci, waɗanda suka laƙuke rayuka da dama, baya da garkuwa da mutane.

Sapi’i Sambo, ya bayyana cewa  ‘‘An sanar da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro game da kisan gillar da aka yi wa Usama.

“Muna yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi a wannan yankin, amma ga shi duk da kasancewansu a nan ’yan fashin daji sun shigo sun kashe Usama.

“Muna roƙon Gwamnatin Tarayya ta ƙaro mana jami’an tsaro domin daƙile wadannan miyagun ayyuka.

“Gaskiya muna cikin damuwa kuma muna matukar bukatar ƙarin jami’an tsaro.”

Zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan labari dai babu wani bayani daga rundunar ’yan sandan jihar.