Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi wa manona da masunta aƙalla 15 yankan rago a yankin Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kulawa ta Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa mayaƙan na ISWAP sun kutsa yankin ne bayan zagargaza da tarwatsa sojoji suka yi wa maɓoyarsu da ke Dajin Sambisa.
Shaidu sun bayyana cewa a ranar Laraba da manoman da masunta suka tafi gonakinsu da wurin yin su ne suka yi arba da mayaƙan ƙungiyar da suka yi musu kisan gilla.
Sun bayyana cewa dai da mayaƙan suka tafi da manoman zuwa ƙauyen Malam Karanti, da suka kwace, sa’annan sun yi musu yankan rago.
- Jami’an tsaro sun daƙile harin Boko Haram sun kashe mayaƙa 5 a Borno
- Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas