Dan Majalisar Jihar Neja mai wakiltar mazabar Magama, Suleiman Musa Nasko, ya sha ruwan duwatsu a hannun mutanen mazabarsa a ranar Asabar.
An kai masa harin ne lokacin da ya je ziyarar jaje ga iyalan da aka kashe yayin harin ofishin ’yan sanda na garin Nasko a makon da ya gabata, inda aka kashe mutum shida.
- Masu garkuwa da mutane sun tsare shi suna zukar jininsa suna sayarwa
- Harin sojojin sama ya hallaka shugaban ISWAP, Sani Shuwaram, a Borno
Lamarin ya faru ne lokacin da wasu fusatattun matasa suka yi masa ihun ba-ma-so, sannan suka jefi ayarin motocinsa.
Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa dan majalisar ya ziyarci fadar Dagacin garin Auna, lokacin da matasan suka fara ihun cewa daga wa’adi daya ba zai kara ba, lamarin da ya haifar da taho-mu-gama tsakaninsu da magoya bayansa.
Majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce amma dan majalisar ya tsira ba tare da an ji masa ko kwarzane ba, saboda daukin da jami’an tsaronsa suka kai masa.
Ya ce lamarin ya faru ne lokacin da Suleiman Nasko ke kokarin barin garin.
“Rashin fahimta ce tsakanin magoya bayan dan majalisar da wasu matasa. Lamarin ya faru ne a garin Auna, inda dan Majalisar ya je ziyarar jaje ga daya daga cikin ’yan sa-kan da aka kashe tare da jami’an tsaro a Nasko.
“Muna kan hanyar fita ne wasu matasa suka fara ihun ba-ma-so, wanda hakan bai dadada wa magoya bayan shi ba. Ko lokacin da ya ji cewa an yi taho-mu-gama, bai ji dadi ba.