✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa daliban Kano karin kudin tallafin karatu da kashi 50

Za a fara biyan kudin tallafin karatun da aka kara nan ba da jimawa ba.

Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa dalibai ’yan asalin jihar karin kashi 50 cikin 100 na kudaden tallafin karatu da take ba su.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da hakan tare da cewa nan ba da jimawa ba za a fara biyan daliban sabon kudin tallafin karatu da aka kara.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wurin laccar cikar Najeriya shekara 61 da samun ’yanci, inda ya samu wakilcin Kwamishinan Yada Labaran Jihar Kano, Muhammad Garba.

Garba, ya ce karin kudin tallafin karatun ya yi daidai da tsarin gwamnatin jihar na samar da ilimi kyauta kuma dole.

Don haka ya roki daliban jihar da su dage wajen ganin sun ci moriyar damar da suka samu wajen neman ilimi mai amfani.