✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi jana’izar mutum 6 da ’yan bindiga suka kashe a Zangon Kataf

An kashe mutanen ne da safiyar Talata a yankin

A safiyar Laraba ce shugaban Karamar Hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna, Francis Sani ya jagoranci jana’izar wasu mutane shida da ’yan bindiga suka kashe a yankin.

An dai kashe mutanen ne yayin wani harin ’yan bindiga a yankin Takanai, da ke mazabar Gora a Karamar Hukumar da misalin karfe 8:30 na daren Talata.

 

A yayin harin dai, an raunata wasu mutane shida baya ga kisan mutum shida da su ka yi.

Da yake yi wa Aminiya karin haske, mai bai wa Shugaban Karamar Hukumar shawara kan harkokin yada labarai, Yabo Chris Ephraim, ya ce shugaban karamar hukumar, Francis Sani da ya kai ziyarar jaje a safiyar Laraba.

Shugaban ya kuma roki mutanen garin da su kwantar da hankulansu daga masu kokarin yamutsa hazo a yankin su ci gaba da zama lafiya.

Ya ce shugaban ya jawo hankalin mutanen Karamar Hukumar da su guji aikata duk wani abu da zai rika ruruta wutar rikici a yankin.

Ya kuma yaba wa jami’an tsaron yankin bisa ga kokarin da su ke yi, inda ya kara jawo hankalinsu da kada ayyukan bata gari ya karya musu gwiwa kan kokarin da suke yi.

Mutanen da a ka yi jana’izarsu sun hada da Sarah Adamu da Rejoice Adamu da Enoch Adamu da Juan Aminu da Salomi Aminu da kuma Meshak Aminu, yayinda wadanda suka samu raunuka suka hada da Kubai Adamu da Judith Adamu da Abigail Adamu da Dennis Joseph da Grace Bitrus da kuma Adamu Ibrahim.

%d bloggers like this: