✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar matukin jirgin saman da ’yan fashin daji suka harbo

An yi jana’izar a masallacin Ɗanja da ke Tudun Wada Zariya

An gudanar da jana’izar matukin jirgin saman sojin Najeriyar nan da aka harbo a dajin jihar Neja, marigayi Flight Lieutenant Ibrahim Adamu Abubakar.

Jana’izar wadda aka gudanar a masallacin Juma’a na Haruna Danja da ke unguwar Tudun Wada a Zariya, limamin masallacin, Sheikh Muhammad Sani Gumi, ne ya jagorance ta.

An gabatar da sallar ne da misalin karfe 12:00 na rana ranar Talata inda wasu dakarun sojan sama suka yi wa gawar rakiya.

Wakilin Aminiya ya rawaito cewa daruruwan jama’a ne da suka hada da maza da mata, ’yan uwa da abokan arziki tare da jami’an Rundunar Sojan Sama ta Najeriya da suka kawo mamacin ne suka halarci sallar jana’izar.

Marigayi Flight Lieutenant Ibrahim Adamu Abubakar ya rasu ne a ranar Litinin din makon jiya, kuma shi ne matukin jirgin saman mai saukar angulu watau MI-171 wanda ke aikin ceton sojoji a lokacin da suka yi karon-batta da ’yan fashin daji a kauyen Chukuba da ke jihar Neja.

Da yake zantawa da ’yan jarida a Zariya, yaya ga mamacin, Abubakar Adamu, ya ce tun a ranar Alhamis, ’yan uwan marigayin suka gabatar da sallar jana’iza ta nesa (Salatul Gha’ib) wadda ake yin ta ba tare da gawa ba.

A cewar shi, sun ɗauki wannan matakin ne sakamakon rashin samun gawar dan uwansu nasu da farko.

Ya ci gaba da cewa, yanzu kuwa da rundunar soja ta sanar da su cewa sun samu gawar kuma zasu kawo masu ita, shi ya sa suka ce a gudanar da sallar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

A wata tattaunawa ta daban da mahaifiyar marigayin, Hajiya Aishatu Adam ta ce dan nata wadda yana daya daya daga cikin yara 27 da aka haifa a gidan, mahaddacin Alkur’ani mai girma ne, kuma ya kasance mutum na gari a duk tsawon rayuwarsa.

Mahaifiyar ta ce marigayi Ibrahim, “Yaro ne mai shiru-shiru, ga biyayya da girmama na gaba da shi.

Marigayin dai ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya biyu.