An jikkata mutane da dama bayan dauki-ba-dadi da aka yi tsakanin magoya bayan wasu sarakuna ’yan uwan juna da aka dakatar a Masarautar Sansani da ke Jihar Taraba.
Aminiya a samu labarin cewa an yi ta harbe-harbe tare da kona gidaje masu yawa a rikicin da ya barke ranar Talata da dare har zuwa safiyar Laraba a Karamar Hukumar Gassol ta jihar ta Taraba.
- Yadda Matsalar Shaye-Shaye Ta Zama Ruwan Dare A Najeriya
- An je kotu nema wa Buhari wa’adin mulki na uku
Rikicin ya barke ne bayan Gwamnatin Jihar ta sauke wani sarki mai daraja ta uku, Abdulmudallabi Muhammed ta maye gurbinsa da dan uwansa, Gide Muhammed a matsayin mai rikon kwarya.
Hakan dai bai yi wa sau magoya bayan basaraken da aka dakatar dadi ba.
Bayan dan lokaci kuma sai gwamnatin jihar ta sauke Gide, ta maye gurbinsa da wani babban basarake a matsayin mai kula da yankin.
A kan haka ne magoya bayan Gide suka fusata suna zargi bangaren Abdulmudallabi da yi makarkashiyar da aka sauke Giden, har ta kai ga ba wa hamata iska tare da jikkata mutane da dama da kone-kone.
Majiyarmu ta ce wasu daga cikin magoya bayan sarakunan da aka sauke sun kwashe iyalansu sun bar yankin saboda gudun abin da zai iya biyowa bayan zaman dar-dar din.
Mun tuntubi mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, amma ya ce bai samu cikakken bayanin abin da ya faru daga babban ofishinsu da ke Karamar Hukumar ta Gassol ba tukuna.