Sama da jiragen alfarma 20 na manyan baki ne suka sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, don halartar auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Nasiru Ado Bayero, a garin Bichi.
Wannan na zuwa ne yayin da manyan mutane a daga duk fadin kasar nan da waje suka yi dafifi domin shaida daurin auren.
Wani jami’i a tashar jirgin saman da ke birnin Kano, ya shaida wa Aminiya cewa jiragen alfarmar mallakar wasu manyan mutane ne da suka halarci shagalin bikin.
A cewar majiyar, halartar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi daga Yola ya kara wa bikin armashi.
“Shugaban Kasa shi ne na karshen isowa, na hangi jiragen alfarma 20 zuwa 30, amma dai ban kirga yawansu ba,” inji shi.
Majiyar ta kara da cewa ana sa ran zuwan wasu jiragen alfarma guda hudu, a daidai wannan lokaci da ake hada wannan rahoto.
Wani bidiyo da ya zaga kafafen sa da zumunta, ya nuna wasu tarin jiragen alfarma da suka isa filin jirgi na Malam Amni Kano don halartar auren da na miji daya tilo ga shugaba Buhari.
Daga cikin fitattun mutanen suka halarci bikin auren sun hadar da tsohon shugaban kasar Najeriya da Nijar, Goodluck Ebele Jonathan da Muhamadou Issoufu.
Sauran sun hada da mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da sauran wasu da dama.