Rundunar ‘yan sandan jihar Kuros Ribas ta tabbatar da yin garkuwa da shugaban kungiyar kwadago na jihar Ben Ukpepi, a gidansa da ke Karamar hukumar Akpabuyo ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Irene Ugbo, ne ya bayyana hakan a yau Laraba yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin labarai a Kalaba babban birnin jihar.
DSP Irene Ugbo, ya ce an yi garkuwan da Ben, ne da misalin karfe 7:30 na dare a jiya Talata inda ake zargin wasu ‘yan bindiga da sace shi.