Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa ta tabbatar da sace Sakataren Hukumar Zaben Jihar (NASIEC), Mohammed Abubakar Opu.
Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Rahman Nansel ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Lafiya, babban birnin Jihar.
- An yi garkuwa da wata mata bayan sa’a 24 da mutuwar mijinta a Katsina
- An kafa kwamitin bincike na musamman kan harin NDA
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, an kai wa rundunar ‘yan sandan jihar rahoton sace sakataren da misalin karfe 1 na ranar 25 ga Agustan 2021.
“An shigar da rahotn cewar wasu ‘yan bindiga su biyar sun shiga gidan sakataren da ke kauyen Bakin Rijiya sannan suka yi garkuwa da shi.
“Tuni kwamishinan ‘yan sanda ya tura kwararrun jami’an ‘yan sanda zuwa yankin don gudanar da bincike,” a cewar sanarwar.
Aminiya ta ruwaito cewa, jami’an tsaro sun bazama wajen domin ceto shi daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da shi.