’Yan bindiga sun yi awon gaba da matar Kwamishinan Kasa da Safiyo na Jihar Binuwai ido na ganin ido.
Masu garkuwar sun tafi da Misis Ann Unenge da karfin tsiya ne a garin Makurdi, kimanin mako biyu bayan an yi garkuwa da wasu matan aure biyu, ciki har da matar wani likita.
Shaidu sun yi zargin ’yan bindigar sun biyo sawunta ne daga hanyarta ta dawowa garin Makurdi daga Daudu inda ta kai wa iyayenta ziyara, suka kuma tafi da ita a motarta kirar Toyota Highlander sabuwar yayi.
Sun ce Misis Ann ta yi kokarin bude kofa ta fito daga motar a daidai ofishin ’yan sanda, sai ’yan bindigar suka fara barin wuta suka razana mutane.
Matar ta yi ta ihu a yayin da masau garkuwa ke tafiya da ita, amma masu suka fizgi motar a guje, suka tsere kafin mutanen da ke wurin su iya yin wani abu.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Binuwai, DSP Catherine Anene ta ce wasu iyalai sun kawo musu rahoton bacewarta amma ba su da rahoton garkuwa da ita.
Ta ce duk da cewa ’yan sanda na zargin garkuwa aka yi da matar, ba su da isassun hujjoji da ke tabbatar da abin da suke zargin.
“Mu dai ce mana aka yi cewa ta bar gida zuwa wani wuri daga nan ba su kara ganin ta ba, saboda haka suka kawo mana rahoton bacewarta,” inji DSP Catherine.