’Yan bindiga sun kutsa cikin wani coci tare yin awon gaba da wasu masu ibada da tsakar daren Lahadi.
Bayan sace mutanen a cocin Cherubim and Seraphim da ke yankin Oba Oko a Karamar Hukumar Ewekoro ta Jihar Ogun, ’yan bindigar sun kira iyalansu suna neman kudin fansa.
- “Juyin mulki”: An tsare shugabannin farar hula na gwamnatin Sudan
- An kama fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Oyo
Iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su sun tabbatar wa wakilimnu cewa masu garkuwar sun bukaci a kawo musu Naira miliyan shida a matsayin kudin fansa.
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ogun ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, Abimbola Oyeyemi.
Ya ce rundunar ta tura jami’anta daga sashen yaki da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa don su ceto mutanen.
Sai dai ya gargadi wuraren bauta da su guji gudanar da tarukan ibada da tsakar dare musamman a wuraren da babu jama’a sosai domin hakan na iya jefa mabiyansu a cikin hadarin fadawa hannun masu satar mutane.