✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Bayelsa

’Yan bindiga sun kai wa Madam Benson hari har gidanta da ke Yenagoa.

Rundunar ’Yan sanda a Jihar Bayelsa, ta sanar da sace mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jihar, Madam Betinah Benson mai shekara 80 a duniya.

Kakakin ’yan sandan Jihar, SP Asinim Butswat ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Yenagoa, babban birnin Jihar.

  1. Sallah: An yi wa fursunoni 136 afuwa a Kano
  2. Yadda tsohuwa ta sace lu’lu’un biliyan N2.4

Bayanai sun ce ’yan bindiga sun kai wa Madam Benson hari har gidanta da ke Yenagoa a ranar Talata da misalin karfe 10 na dare.

SP Butswat ya ce, “Rundunar ’yan sandan Bayelsa ta fara farautar wadanda suka yi garkuwa da Madam Betinah Benson don gurfanar da su.

“Madam Betinah Benson mai shekara 80 an yi garkuwa da ita a ranar 20 ga watan Yuli 2021, da misalin karfe 10 na dare a gidanta da ke titin Azikoro a Yenagoa.

“Yan bindigar sun yi shiga ta kakin sojoji sannan suka sace ta zuwa wani wuri da ba a sani ba.

“Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Mike Okoli da sauran jami’an tsaro sun ziyarci gidan da aka sace ta, sannan ana ci gaba da gudanar da bincike,” a cewarsa.

Sai dai har yanzu Sakataren Gwamnatin Jihar, Konbowei Friday Benson, bai ce komai a kan lamarin ba.

%d bloggers like this: