’Yan bindiga sun yi garkuwa da Dan Majalisa mai wakiltar Mazabar Nguroje a Majalisar Dokokin Jihar Taraba daga gidansa.
Masu garkuwa dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da Barista Bashir Mohammed ne da misalin karfe 1.30 da daren Laraba daga gidansa da ke unguwar Yama Sala a garin Jalingo.
- Asirin budurwa ya tonu bayan saurayi ya yi garkuwa da ita
- Gwamnati na leken asirin wayoyin ’yan Najeriya —Rahoto
- Ya yi tattakin kilomita 450 bayan sa-in-sa da matar sa
- Jama’ar gari sun yi wa dan fashi dukan kawo wuka
Shaidu sun ce kusan mutun 20 ne suka yi dirar mikiya a gidan dan majalisar suna barin wuta na kusan minti 45 kafin su tisa keyarsa ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba.
Makwabta sun shaida wa Aminiya cewa maharan sun shafe tsawon lokaci a gidan dan majalisar, har suka kamo shi da karfin tsiya a dakinsa suka sa shi a motarsu suka bar unguwar a sukwane.
Da yake tabbatar da aukwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce tun rundunar ta fara aiki don ceto dan majalisar.
Bashir Mohammed shi ne dan majalisan na biyu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a Jihar Taraba.
A shekarar 2017 ’yan bindiga sun sace wani Dan Majalisa Hosea lbi a gidansa da ke garin Takum kuma suka kashe shi bayan sun karbi miliyoyin Nairori a matsayin kudin fansa.