✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da daliban Islamiyya a Katsina

Daliban sun dawo daga wajen bikin Maulidi ne, lokacin da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Rahotanni daga Karamar Hukumar Dandume ta jihar Katsina sun tabbatar da wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makarantar Islamiyya da dama a garin a daren ranar Asabar.

Harin dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan sako daliban makarantar sakandiren Kankara sama da 300 duk dai a jihar ta Katsina da su ma aka yi garkuwar da su.

Wata Jaridar intanet mai suna ‘Katsina Post’ wacce ta ruwaito faruwar lamarin ta ce an sace ne daliban ne a yankin Mahuta a karamar hukumar Damdume, bayan sun taso daga wajen bikin Maulidi a wani kauye da ake kira Unguwar Al-Kasim.

Sai dai ya zuwa yanzu ba a san adadin daliban da aka yi garkuwa da su ba.

Jaridar ta rawaito cewa kakakin ‘yan sandan Katsina SP Gambo Isa, bai ce komai akan lamarin ba sakamakon ya tafi halartar wani taro.

Daga bisani dai Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na Jihar Katsina ya tabbatar da ceto daliban da ma karin wasu mutum hudu daga hannun maharan bayan samin koke daga mazauna yankin.