Dalibai Amurkawa kimanin su 40 daga kungiyar Morehouse College Glee Club da ke Atlanta a kasar Amurka, aka yi bikin rada musu sunan gargajiya na kabilar Ibo bayan da suka gano cewa kabilar ce asalinsu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, yayin taron radin sunan, daliban sun ba da labarin yadda suka bi diddigin gano asalin nasu ta hanyar yin gwajin kwayar halitta na DNA.
- ’Yan Ta’adda Sun Kashe ’Yan kasar China da ’yan sanda a wurin hakar ma’adinai
- Kotu ta raba aure saboda masifar mata
Sarkin kauyen Ibagwa-Aka da ke yankin Karamar Hukumar Igbo-Eze ta Kudu a Jihar Enugu, tare da Mai Martaba Igwe Hyacinth Eze, su ne suka jagoranci bikin radin sunan.
Sarakunan da ma sauran al’ummar yankin sun yi matukar murna da gano asalinsu da daliban suka yi.
Wasu daga cikin sunayen gargajiyar Ibo da aka zana wa wadanda lamarin ya shafa sun hada da; Ezuomike da Ogalanya da Odenigwe da Anyim da Ifeanyi da sauransu.
Jami’in Hulda da Jama’a na Ofishin Jakadancin Amurka da ke Legas, Stephen Ibelli ya ce, yana daga dalilan ziyarar kungiyar a Najeriya bikin cika shekara 50 da ziyarar farkon da kungiyar ta kawo Najeriya a 1972.
Kazalika, ya ce kungiyar za ta kai ziyara a Abuja da Enugu da kuma Legas don karfafa kawancen al’adun Amurka da Najeriya ta hanyar wakoki da finafinai da sauransu.
Taron radin sunan ya samu halartar baki na kusa da nesa, ciki har da sarkunan garjiya, jam’ian gwamnati da ma ‘yan siyasa.