Sabbin sojoji 4,918 da suka sami horo daga makarantar horas da kuratan soji ta Najeriya (Depot) da ke Zariya ne aka yaye a wani buki mai kayatarwa da aka gudanar a filin fareti na Kim Hamma da ke barikin.
Da yake jawabi ga sabbin sojojin, Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, Wanda Laftanar Janar Lamidi Adeosun, Babban bako Laftanar Janar Lamidi Adeosun, Babban Jami’i Mai Kula da Tsara Manufofi a Hedkwatar Rundunar Sojin Kasa, ya wakilta.
ya bayyana farin ciki cewa sabbin dakarun sojin da aka yaye a shirye suke domin fuskantar dukkanin wasu kalubale da ke damun kasar nan.
Buratai ya yi jawabin ta bakin Laftanar Janar Lamidi Adeosun wanda ya wakilce shi a wurin bikin.
Laftanar Janar Lamidi Adeosun, Babban Jami’i Mai Kula da Tsara Manufofi a Hedkwatar Rundunar Sojin Kasa, ya wakilta.
A jawabinsa, ya ce tun sadda aka kafa makarantar horas da kuratan sojin a shekarar 1924 take cika manufar kafa ta ta ba da horo da kuma cusa kwarewa ga ‘yan Najeriya domin su samu dabarun kishin kasa da kare ta daga dukkanin wata barazana.