✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa ’yan daba 106 hukunci a kwana 10 a Kano

An yanke wa ’yan daba 106 hukunci ba tare da zabin biyan tara ba a kwanaki 10 Jihar Kano

A cikin kwanaki 10 kotu ta yanke wa ’yan daba 106 hukunci ba tare da zabin biyan tara ba a Jihar Kano.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar cewa a cikin kwanaki goman, kotu ta kuma ba da umarnin tsare karin wasu ’yan daba 43 a gidajen kangararrun yara.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna  Kiyawa, ya kara da cewa laifukan da kotu ta kama ’yan daban da su sun hada da kisa, fashi da makami, raunata jama’a da kuma sace mutane.

Kiyawa ya bayyana cewa wannan ya faru ne a cikin kwanaki 10, daga 24 ga watan Yuni zuwa 4 ga Yuli, 2024.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya yana wa bangaren shari’a bisa rawar da ya taka wajen samun wannan nasara.

Sannan ya yi kira ga al’umma da su rika ba wa ’yan sanda hadin kai da bayanai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a Jihar Kano.