✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa ’yan bijilanti 5 hukuncin rataya a Kano

Kotun ta yanke musu hukuncin dauri na tsawon shekaru biyu kan laifin hadin baki.

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 1 da ke Sakatariyar Audu Bako, ta yanke wa wasu ’yan bijilanti biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An dai yanke musu hukuncin ne bayan samunsu da laifin kisan wani matashi dan shekaru 17 mai suna Ahmad Musa a unguwar Sabon Titin Panshekara.

Masu laifin sun hada da Emmanuel Korau da Eliesha Ayuba Jarmai da Irimiya Thimothy da Auwalu Jafar da Mustapha Haladu.

An dai soma tuhumar ’yan bijilantin da laifuka biyu na hadin baki da kuma kisan kai, laifukan da suka saba da sashe na 97 da 221 na Kundin Pinal Kod.

Sai dai a yayin sauraron shari’ar duk sun musanta aikata laifukan da ake zargin su da shi.

Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin sauraron shari’ar ce lauyan mai kara, Barista Lamido Sorondinki ya gabartar wa kotu shaidu biyar.

Shi ma lauyan wadanda ake kara, Barista Ahmad Muhammad ya gabatar wa kotu shaidu shida ciki har da wadanda ake kara.

Yayin da take yanke hukunci, Alkalin Kotun kuma Babbar Jojin Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki ta bayyana cewa kotun ta gamsu da hujjojin da mai kara ya gabartar wa kotu, wanda ta yi amfani da su wajen yanke hukunci.

Ta bayyana cewa game da laifin kisa, kotun ta yanke wa wadanda ake kara hukuncin kisa ta hanyar rataya. Haka kuma, game da laifin hadin baki, kotun ta yanke musu hukuncin dauri na tsawon shekaru biyu a gidan gyaran hali.

Ana iya tuna cewa, tun a ranar 22 ga watan Janairu 2022 ’yan bijilantin su biyar suka hadu suka yi amfani da gorori suka yi wa marigayin dukan kawo wuka, da bisani kuma wanda ake kara na farko ya yi amfani da wuka ya daba wa marigayin a wuyansa.

Daga baya ’yan bijilantin suka dauki gawar marigayin zuwa ofishinsu da ke Cibiyar Horar da Matasa ta Sani Abacha.

Bayan wani lokaci kuma aka dauke shi zuwa ofishin ’yan sanda na Kuntau, wanda su kuma suka kai shi Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed, inda aka tabbatar da rasuwarsa sakamakon raunukan da ya samu a wuyansa da kuma kansa.