Kotu ta yanke wa tsohuwar Shugabar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, mai shekara 77 hukuncin daurin shekara uku da kuma aiki mai tsanani, saboda laifin magudin zabe.
Kotun ta yanke mata hukuncin ne bayan samun Suu Kyi, wadda sojoji suka kifar fa gwamnatinta, da laifin murdiyar zaben da ta ba ta gagarumar nasara a shekarar 2020.
- Masu Twitter za su fara iya yin gyara bayan sun wallafa sako
- Muhimman Abubuwa Kan Sheikh Dahiru Bauchi
A safiyar Juma’a kotu ta, “Yanke mata hukuncin daurin shekara uku da kuma aiki mai tsanani,” in ji majiyar kamfanin dillancin labarai na AFP, wadda ta ce Suu Kyi na cikin koshin lafiya a lokacin da ta halarci zaman kotun.
Tun a shekarar 2021 sojoji ke tsare da dattijuwar, bayan sun kifar da gwamnatinta, inda daga bisani wata kotun soji ta yanke mata hukuncin daurin shekaru 17 kan laifin almundahana.
Sojojin kasar sun yi zargin cewa an aikata gagarumin magudi a zaben na 2020, wanda jam’iyyar Suu Kyi ta NLD ta lashe.
Sai dai masu sanya ido na kasashen duniya sun ce akasarin zaben na 2020 an shi ba tare da magudi ba a Myanmar.
Tuni dai sojojin kasar suka soke sakamakon zaben, wanda suka ce sun gano an yi magudi sama da sau miliyan 11.
A wani jawabi da ya yi a watan Agusta, jagoran gwamantin sojin, Min Aung Hlaing, ya ce za a gudanar da zabe idan aka samu ‘aminci da daidaito’ a kasar, amma bai ayyana lokaci ba.
Kungiyoyin sanya ido a kasar Myanmar sun ce an kashe akalla 2,200 wasu 15,000 kuma na tsare a hannun sojoji, saboda mutanen sun fito zanga-zanga, bayan sojojin sun yi juyin mulki.