Wata kotu da ke gundumar Kollam a Jihar Kerala ta Indiya ta yanke wa wani matashi da ta samu da laifin yin amfani da maciji wajen hallaka matarsa hukuncin kisa har hawa biyu.
Masu shigar da kara sun bayyana hukuncin kotun wanda aka yanke ranar Laraba a kan wani mai suna Sooraj Kumar, mai kimanin shekaru 28 da cewa ba kasafai ake yanke irinsa ba.
- Najeriya a Yau: Shin Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Zai Kawo Karshen Magudin Zabe?
- An sako 3 daga cikin daliban da aka sace a Kudancin Kaduna
Masu shigar da kara a Kudancin Jihar ta Kerala sun ce Sooraj ya jefa wa matar tasa mai suna Uthra macijin ne wanda ya dauko hayarsa daga wajen masu wasa da maciji, bayan ta shafe kusan wata biyu tana jinya a asibiti.
A cewar su, bayan ta sami sauki ne sai ta ci gaba da jinyar a gidan iyayenta, amma Sooraj ya zo da macijin har gidan surukan nasa sannan ya jefa mata shi lokacin da take bacci.
Macijin mai dauke da dafi dai ya sassareta, sannan ya kasheta a watan Mayun 2020.
An dai kama shi ne a gidansa a baran, bayan da iyayen matar suka yi zargin cewa an sha kai mata hari saboda a kwashe sadakin aurenta.
Iyayen nata sun kuma yi zargin cewa bayan mutuwar Uthra, mijin nata ya yi kokarin yin baba-kere a kan dukiyarta.
Sai dai a yayin yanke hukuncin, kotun ta ce ta sami Sooraj da laifin aikata kisan kai da kuma sanya wa matar guba, bayan da a baya ya taba kokarin hallaka ta da maciji.
Alkalin kotun, Mai Shari’a M. Manoj ya yanke wa wanda ake zargin hukuncin kisa har hawa biyu, sannan ya yi fatali da bukatar yi masa sassauci saboda shekarunsa.
Sooraj dai ya musanta aikata laifin, amma ’yan sanda sun ce wasu bayanai da aka tattara daga wayarsa ta salula sun nuna cewa ya yi hulda da masu sana’ar maciji kuma ya kalli wasu hotunan bidiyo na macizai a intanet kafin ya aikata laifin.