Wata kotun yaki da ta’addanci ta yanke hukuncin kisa kan wasu masu tsattsauran ra’ayin Islama biyar kan kisan wani marubuci kusan shekaru shida da suka gabata a birnin Dhaka na kasar Bangladesh.
Lauya mai shigar da kara, Abdullah Abu ya ce kotun mutanen da aka yanke wa hukuncin saboda laifin kashe wani marubuci kuma lauya haifaffen Amurka mai suna Avijit Roy, kotun ta yanke wa mutum na shida hukuncin daurin rai-da-rai.
Ya ce kotun ta samu mutum na shidan ne da laifin tunzura kisan ta hanyar sakonnin da aka yada a shafukan sada zumunta, sauran kuma ta same su da hannu kai tsaye a kisan.
Mahara sun yi wa Roy kisan gilla tare da raunata matarsa yayin da ma’auratan ke dawowa daga baje kolin littattafai a Dhaka a ranar 26 ga Fabrairu, 2015.
Kafin nan sun yi tafiya zuwa Amurka don halartar bikin kaddamar da sabon littafin Roy ya wallafa a wani baje koli.
Lauyan ya ce an tabbatar da laifin mutanen aka kuma an yanke musu hukunci mafi girma, yayin da ragowar mutum biyu da ake zargi ke ci gaba da buya.
Lauyan da ke kare wanda ake kara, Faruq Ahmed ya ce wadanda yake karewa za su daukaka kara kan hukuncin zuwa babbar kotu.
Roy, wanda ya kirkiro wani sanannen shafi, Muktomona, ya yi rubuce-rubuce kan kimiyya, zamantakewa da falsafa a kasar ta Asiya ta Kudu da ta fi yawan Musulmi.
Ya wallafa wasu littattafai masu rikitarwa ciki har da Samakamita (Luwadi) da Obiswasher Darson (Falsafar marasa imani da samuwar Allah).
Bangladesh mai rinjayen Musulmai ta fuskanci hare-hare kan marubutan kananan addinai masu rubutun ra’ayi a intanet da suak hada da malamai da mutane daga addinai marasa rinjaye daga 2013 da 2016.
Kungiyar masu da’awar kafa daular Musulunci da kungiyar al-Qaeda da kungiyoyin da ke karkashinta sun sha yin ikirarin kai hare-haren.
Amma masu bincike a kasar sun ce mayaka yan asalin kasar ne ke da alhakin kai hare-haren.