A ranar Talatar da ta gabata ce jaridar El-Mundo da ake wallafa ta a Sifen ta ruwaito cewa dan wasan baya a kulob din Real Madrid na Sifen, Marcelo ya amince da hukuncin da wata kotu a Sifen ta yanke masa bayan ta same shi da laifin yin magudi wajen biyan kudin haraji da aka kiyasta sun kai Rsh miliyan 87.1. Kotun dai ta yanke masa hukuncin daurin wata 4 a gidan yari ko kuma ya biya tarar Rsh miliyan 87.1.
Yanzu Marcelola ya shiga jerin wadanda aka taba samu da laifin kin biyan haraji a kasar Sifen.
Sauran wadanda aka taba samu da kin biyan haraji a Sifen sun hada da tsohon kocin kulob din Real Madrid Jose Mourinho da Cristiano Ronaldo da Aledis Sanchez da Lionel Messi da sauransu.
Sai dai kamar yadda hukuncin ya nuna, Marcelo zai biya haraji ne hade da tara ba tare da ya shiga gidan yari ba. Dokar ta nuna duk wanda bai biya harajin da bai wuce shekara biyu ba, to ba zai shiga gidan yari ba, sai dai ya biya harajin da tarar da aka yi masa.
Marcelo dai an same shi ne da laifin yin coge wajen biyan haraji inda ya hada baki da wani kamfani a Uruguay mai suna Brisen Trade SA ta hanyar tallata Marcelola ba tare da sani ko izinin hukumomin Sifen ba.
A lokacin da ake tuhumarsa game da wannan batu a gaban kotun, Marcelo ya amince da hukuncin da aka yanke masa na wata 4 a gidan kaso ko biyan tarar Rsh 87.1.
Sai dai dan kwallon ya nemi sassaucin biyan kashi 40 daga cikin 100 na harajin, kuma kotun ta amince.
Idan za a tuna, Cristiano Ronaldo ya biya haraji da tarar da aka yi masa a lokacin da hukumar kwallon kafa ta Sifen ta same shi da laifin kin biyan haraji. Ana ganin haka na daga cikin dalilan da dan kwallon ya canja sheka zuwa kulob din Jubentus na Italiya a karshen kakar wasan da ta gabata.
Lionel Messi dan kwallon FC Barcelona ma ya taba yin haka a baya, inda aka yanke masa hukuncin daurin wata 18 a gidan yari amma ya biya tarar ba tare da ya shiga gidan kaso ba.