✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An umarci wadanda suka mallaki makamai a Kano su mika su ga ’yan sanda

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta umarci dukan wadanda suka mallaki makamai ba bisa ka’ida ba a jihar su hanzarta mika su gare ta daga…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta umarci dukan wadanda suka mallaki makamai ba bisa ka’ida ba a jihar su hanzarta mika su gare ta daga nan zuwa ranar 27 ga watan nan na Maris.

Wata takarda da rundunar ta fitar dauke da sa hannun Kakakin Rundunar DSP Magaji Musa Majiya ta bayyana cewa daukar wannan matakin ya biyo bayan umarnin da Sufeton Janar na ’Yan sandan Najeriya, Ibrahim K. Idris ya bayar ne a kan haka.

Rundunar ta ce “Wannan ya shafi kungiyoyin ’yan banga (bijilanti) da kungiyoyin sa-kai don taimakon al’umma da duk wata kungiya da ke aikin samar da tsaro da Gwamnatin Tarayya ba ta sahale musu ba da kuma suke da makamai a hannunsu da su mika su ga rundunar ’yan sandan,” inji shi.

A cewar sanarwar makaman da ake neman jama’a su mika sun hada da nau’o’in bindiga da duk wani abu mai kama da bam da sauran bindigogin da aka kera su a gida.

Sanarwar ta ce za a mika makamakan ne ga ofisoshin ’yan sanda da ke kusa ko kai-tsaye a kai ga hedikwatar ’yan sandan jihar da ke Bompai ga kwamitin da aka kafa don karbar makaman a karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda na jihar kafin lokacin.

Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar su kai karar duk wanda suka san ya mallaki miyagun makamai da kuma bai sallama su ga rundunar ba.