Jami’an jinya a Babban Asibitin Suleja a Jihar Neja sun shiga damuwa bayan da aka kai musu wata mata da wani mai mota ya kade ya gudu ya bar ta a yashe.
Ma’aikatan wadanda suke ci gaba da aikin jinkai ga wannan baiwar Allah da ke fama da raunukan da suka hada da karaya, sun ce an tsince ta a yashe bayan mota ta kade ta a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Wani da ke aikin sa-kai don kula da marasa lafiya a asibitin mai suna Malam Ibrahim Ali, ya ce bayan jami’an Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC) sun kai matar asibitin a ranar wata Alhamis mako uku da suka gabata da misalin karfe 8:30 na dare, an gano raunuka a jikinta da suka hada da kai da kujewa a gwiwoyinta biyu, sai kuma karaya biyu a hannuwanta.
Ya ce matar ba ta iya magana, hatta abinci sai an yi mata dure ta baki, sannan sai an sa mata roba a janye mata fitsari.
Malam Ibrahim Ali ya ce shi da wadansu daga asibitin sun zaga wasu kauyuka da ke kusa da inda aka tsince ta suka sanar da shugabannin wuraren don gano danginta amma ba a samu nasara ba.
Wani jami’in FRSC a garin Zuba, Abdullahi Haruna ya ce bayan faruwar lamarin wadansu sun buga wa ofishinsu waya, su kuma suka dauko ta suka kai ta asibitin da ake jinyarta.