An tsinci wani jariri sabuwar haihuwa a lullube da zani a kusa da wani kango da ke Unguwar Mu’azu a jihar Kaduna, a ranar Asabar.
Wani mutum ne dai ya tsinci jaririn wanda kuma daga bisani ya mika shi ga ’yan Kungiyar Sintirin ta Jihar, watau KADVs.
- Mahara sun kashe basaraken Fulani da ’ya’yansa 4 a Zariya
- Yadda a tarihi aka yi kokarin sace gawar Manzon Allah (SAW)
Jaririn dai an tsinci shi ne babu ko riga a jikinsa sai famfas da aka saka masa.
Sai dai ba a san wanda ya ajiye shi ba, ko kuma lokacin da aka kai shi wajen.
Wani jami’i wanda wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “A kusa da wani kango muka tsince shi, amma yana cikin koshin lafiya kuma tuni mun sanar da ofishin ’yan sandan Kabala.”