✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe basaraken Fulani da ’ya’yansa 4 a Zariya

Bayan kisan, maharan sun kore shanunsa sama da 100

Wasu Mahara sun kai hari gidan Ardon Birni da kewayen Zariya, Alhaji Shuaibu Mohammed inda suka halaka shi tare da yayansa guda 4 a daren Asabar.

Mai dakin marigayin, Mallama Halima Shu’aibu ta sanar da manema labarai cewa Maharan su 5 ne kuma sun fada masu gida ne da misalin karfe 10:00 na dare sannan suka tafi dakin Ardon inda suka kashe shi.

A cewarta daga nan ne sai suka bi daki-daki na ’ya’yan nasa su hudu, dukkansu magidanta, suka halaka su.

Matar ta bayyana sunan ’ya’yan da aka kashe da suka hada da Adamu Shuaibu, Musa Shuaibu, Abubakar Shuaibu da kuma Haruna Ibrahim.

Halima ta kara da cewa bayan sun kammala kisan, sai kuma suka kora shanunsu kimanin guda 100.

Shi ma da yake magana da manema labarai, daya daga cikin ’ya’yan Ardon da ya rage, Abdurrahman Shuaibu ya ce bayan sun gama da gidansu, maharan har ila yau sun kuma harbi mutane biyu a kan hanyarsu ta barin kauyen.

Da Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce zai tuntubi babban jami’in ’yan sanda na Zariya don kin cikakken bayani yadda abin ya faru.

Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton bai kira don tabbatar da labarin ba.