Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) ta gano gawar budurwar nan mai suna Aishat wadda ruwan sama ya yi sanadiyar hallaka ta.
Babban Daraktan Hukumar ta LASEMA Olufemi Oke-Osanyintolu ya ce an gano gawar Aishat ne a ranar Talata 23 ga watan Yuni kwana guda bayan da ta zurma a wani rami a yankin Surulere inda daga nan ruwa ya tafi da ita.
Ya ce tun bayan sadda ruwan ya tafi da budurwar mutanen unguwar da jami’an hukumar suka dukufa domin ceto ranta, sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba, inda aka tsinci gawarta kwana guda da faruwar lamarin a wani rami cikin magudanar ruwan.
“Da misalin 12.30 na ranar Litinin ruwan ya tafi da ita, tun daga lokacin jami’anmu da jama’ar unguwa suka yi ta aiki don ceto ta.
- Ana ci gaba da neman yaran da ruwan sama ya tafi da su
- Ambaliyar ruwa ta raba mutum 300 da gidajensu
“Ba a yi nasarar haka ba sai a ranar Talata muka yi gano gawarta a ramin magudanar ruwan. Al’ummar unguwar sun binne ta a kusa da magudanar ruwan”, inji shi.
Ambaliya bayan ruwan saman tamkar da bakin kwarya da ya sauka a Legas a ranar Litinin ne ya yi sanadiyar mutuwar budurwar bayan ya janye ta a kan hanyarta ta zuwa gida a yankin Alapafuja.
Ko a daminar bara ma a jihar Legas ruwan sama ya tafi da wata budurwa da ke bisa babur na dan acaba alokacin da mai babur din ya kauce hanya ya fada magudanar ruwa a yankin Iyana-Paja.
Daminar bana a Legas ta faro ne da yin ambaliyar ruwa a gidajen jama’a inda ruwa yake malala a manyan tituna tare da cin gidaje, lamarin da ya sa a makon jiya da yawa daga cikin mazauna suka yi ta fama da kwalfar ruwan da ya shiga gidajensu.
Masana na alakanta matsalar da rashin kyakkyawan tsarin kwashe shara, inda sau tari akan toshe magudanan ruwa da tarin shara, lamarin da ke sa ruwa neman wata hanyar.