Ambaliyar da aka samu sanadiyar mamakon ruwan sama ta kashe aƙalla mutum 33 a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Ruwan saman kamar da bakin ƙwarya ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgar ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin sama.
A gundumar Debonhomme da ke gabashin ƙasar, ruwan ya laƙume motoci da dama, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna ƙasar yin hijira.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa wasu mazauna yankin na yunƙurin hijira ta cikin ruwa da ninƙaya, wasu kuma sun yi amfani da kwale-kwale.
Birnin na da mazauna miliyan 17, wanda ke da maƙotaka da kogin Kongo — ɗaya daga cikin mafiya girma a duniya.
Wasu ɓangarorin birnin na fama da zaizayewar ƙasa, abin da shugaban ƙasar ya ce sauyin yanayi na ƙara ta’azzara lamarin.
BBC ya ruwaito cewa ruwan ya share gidaje da yawa a yammacin Kinshasa ranar Juma’a zuwa wayewar garin Asabar.