✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsige Shugaban Majalisar Jihar Kogi

Ana zargin tsigewar na da nasaba da zargin cin amanar Gwamna Yahaya Bello a zaben dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar APC

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Kogi sun tsige Shugaban Majalisar,  Prince Matthew Kolawole sa’o’i bayan tsige Mataimakin Shugaban Majalisar, Ahmed Muhammed da wasu shugabannin majalisar uku.

’Yan majalisar 19 ne suka sanya hannu kan takardar sanarwar tsige Prince Kolawole, bisa zargin karkatar da kudade sakaci da aiki.

Sun bayyana cewa tun shekarar 2019 shugaban majalisar ke kin biyan su hakkokinsu, baya ga karkatar da kudade da karbar bashi na miliyoyin Naira da sunan Majalisar da sauran na’uikan almundahana.

Haka kuma sun gano yana nadar muryoyinsu a sirrance ya kai wa gwamnan jihar Yahaya Bello, domin neman fada.

Sun bayyana cewa tsige shugaban majalisar ta fara aiki ne daga ranar Litinin, 13 ga watan Yuni da muke ciki.

Shi kuma mataimakin nasa mutum 17 ne suka sanya hannu kan takardar tsige shi.

Amma a martaninsa, Prince Kolawole ya bayyana abin da ’yan majalisar suka yi a matsayin soki-burutsu.

Sakataren Yada Labaransa, Femi Olugbemi ya ce ikirarin ’yan majalisar na tsige Prince Kolawole haramtacce ne, hasali ma akwai wadanda suka sanya hannu a kan takardar da ranar Juma’a aka kawo su da sunan maye gurbin shugabannin majalisar da ake riya cewa an tsige.

Ana zargin wannan sabon rikici na da alaka da kuri’a 47 da Gwamna Yahaya Bello ya samu a zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC inda ya zo na hudu.

Kasancewar daliget 63 Jihar Kogi ke da su a zaben, hakan ya sa ake zargin wasu masu rike da mukamin siyasa da shugabannin jam’iyyar da cin amanar gwamnan a zaben dan takarar.