✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsare wasu mata a gidan yari saboda azabtar da ’yar aiki

Matan sun yi wa ’yar aiki mai shekara 10 wanka da tafasasshen ruwan aika

Wasu mata biyu na tsare a gidan yari bayan da suka yi wa wata karamar yarinya mai shekara 10 wanka da tafasasshen ruwa.

Wata Kotun Majistare ce ta ba da umarnin tsare matan su biyu a gidan yari da ke Onitsa Jihar Anambra, da suka hada da wata mai shekara 22 da dayar mai shekara 34.

Makwabta da ’yan sanda sun ce jikin karamar yarinyar wadda ’yar aiki ce ya sassale sakamakon zuba mata tafasasshen ruwan da matan suka yi saboda ta kasa jiran su ta mayar da bahon ruwan da ta kai musu.

’Yan sanda sun damke matan ne bayan makwabta sun kai karar cin zarafin da suka yi wa ’yar aikin wanda yanzu haka take kwance a asibiti ana jiyar ta.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra, Haruna Muhammad, ya ce yarinyar ta samu munanan raunuka a jikinta sakamakon kunar ruwan zafin da aka zuba mata.

Ya ce Rundunar ba ta yi wata-wata ba wajen cafke su bayan samun korafin abin da suka aikata a garin Ndiowu da ke Karamar Hukumar Orumba ta Arewa a Jihar.

Ya ce an gurfanar da matan a Kotun Majistare na Nanka bayan bincike, amma kotun ta sa a tsare su a gidan yari, ta kuma dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Fabarairu, 2021.

%d bloggers like this: