Jami’an tsaro sun yi awon gaba da Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado.
An tsare Muhuyi Magaji Rimingado ne kan binciken badaƙalar karkatar da Naira biliyan huɗu, a cewar wata majiya a Hukumar.
Majiya wadda ta buƙaci a ɓoye sunanta ta shaida wa Aminiya a ranar Juma’a cewa, “Gaskiya ne an tsare shi, kuma akwai yiwuwar z a tafi da shi Abuja.”
Ta ce, ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin ASP Ahmed Bello, sun ce tilas ne su tafi da Muhuyi Rimingado, saboda umarnin da aka ba su daga sama na yin hakan.
- ’Yan ta’adda na shirin kai hari Kano
- Mun ceto yaran Kebbi 19 da aka yi safararsu zuwa Calabar – NAPTIP
- Tinubu ya ba Ganduje da Gawuna shugabanci a Hukumar Filayen Jirage da Bankin gidaje
Ta ƙara da da cewa tsarewar da aka yi masa na da alaƙa da binciken da ake yi kuma tsohon Shugaban Kamfanin Kayan Gina na Jihar Kano (KASCO), Bala Muhammad Inuwa, wanda ake zargi da karkatar da Naira biliyan huɗu.
A watan Nuwambar shekarar 2023 ne Mai Shari’a Hafsat Yahaya ta Babbar Kotun Jihar Kano ta fara sauraron shari’ar, inda ta ba da umarnin ƙwace wasu kadarori da kuma rufe asusun banki da ke da alaƙa da zargin, har sai ta yanke hukunci.
A watan Disambar shekarar, tsohon shugaban na KASCO, Bala Muhammad Inuwa, ya shigar da wata ƙara a gaban Mai Shari’a A’isha Ya’u ta babbar kotun jihar, yana neman kotu ta ba da umarnin janye ’yan sanda daga harabar Kamfanin Limestone Processing Links Ltd., ind suke tsare da kadarorin, kuma kotun ta ba da umarnin janye jami’an kamar yadda ya nema.
Amma daga bisani Hukumar PCACC ta ɗaga kara da cewa ba ta san da umarnin kotun ba, saboda ba a sanya ta a cikin waɗanda ake ƙara ba a sabuwar shari’ar. Hukumar ta bayyana cewa a matsayinsa na mai alaƙa da lamarin kai tsaye, ya kamata a sanya ta a matsayin wadda ake ƙara, maimakon ’yan sanda su kaɗai.
Sakamakon haka ta shigar da ƙarar neman dakatar da umarnin janye ’yan sandan, tare da neman a shigar da ita cikin jerin waɗanda ake ƙara, saboda gadin kayan kawai aka sa ’yan sanda su yi, amma kayan a ƙarƙashin ikon hukumar suke.
Kimanin makonni biyu da suka gabata Muhuyi Magaji Rimingado ya shaida wa wani taron ’yan jarida wasu na ƙoƙarin kwashe kadarorin, waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan biyu, zuwa Abuja.
Daga baya aka mayar da kadarorin waɗanda suka haɗa da tireloli da manya da ƙananan motoci daga harabar kamfanin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso zuwa ɗakin ajiyar kayayyaki mallakin Gwamantin Jihar Kano a Ƙaramar Hukumar Nassarawa.
Rimingado ya bayyana cewa dokar hukumar ta ba ta ikon tsare irin waɗannan kadarori a yayin da ake ci gaba da shari’ar.
Wasu na alaƙanta tsare Muhuyi Magaji Rimingado da wasu mayan bincike da shari’o’in da hukumar ke yi domin ƙwato kadarorin gwamnati da aka karkatar.
Zuwa lokacin da aka kammala wannan labari babu cikakken bayani game da inda aka kai Rimingado ko halin da yake ciki.