Mahukuntan kasr Sri Lanka sun tsare mutum bakwai ciki hard a daya daga cikin limaman addinin Buddah da ake zargi da kai hari ga wanin ginin Majalisar dinkin Duniya da aka ajiye ’yan gudun hijirar Musulmin Rohingya a makon jiya.
An kama limamin Buddan mai suna Monk Akmeenmana Dayaratana da sauran wadanda ake zargi ne a ranar Litinin da ta gabata, kuma an bayar da umarnin a tsare su har zuwa ranar Litinin mai zuwa, inji Kakakin ’yan sanda Ruwan Gunasekara. Ya ce an kama wadansu mutum biyar tare da tsare su a karshen mako.
An zargi wadansu mutanen Sri Lanka wadanda galibinsu mabiya addinin Buddah ciki har da limaman addinin da ke zanga-zanga da kai hari ga wani ginin majalisar da ke wajen birnin Kolombo inda Musulmin Rohingya 31 ciki har da kananan yara 17 suka yi gudun hijira daga Myanmar a watan Afrilun bana, inda suke samun mafaka.
Limaman Buddah sun jefi ’yan gudun hijirar da ta’addanci inda suka nemi a mayar da su Myanmar, lamarin da ya tilasta ’yan sanda kwashe su daga ginin zuwa wani wuri na daban.
Wani faifan bidiyo da wata kungiyar ’yan kishin kasa mai suna Sinhala National Mobement, ta sanya a shafin Facebook ya nuna masu zanga-zangar suna kiran Musulmin Rohingya “da ’yan ta’adda da suke kashe ’yan Buddah a Myanmar” suna cewa ba za su zauna a Sri Lanka ba.
Mabiya addinin Buddah ne ke da kashi 70 cikin 100 na mutanen kasar Sri Lanka mai mutum miliyan 20, yayin da Musulmi suke da kashi 10.
Fiye da rabin miliyan daya na Musulmin Rohingya ne suka yi hijira daga yankin zuwa Bangaladesh, a fiye da wata daya, lamarin da ya jawo matsalar ’yan gudun hijira mafi muni da ya auku a Asiya a shekarun nan. Kuma tashin hankalin na bayan nan ya auku ne sakamakon harin da ake zargin wata kungiyar Musulmi ta kai wa jami’an tsaro a ranar 25 ga Agusta, lamarin da ya tunzura sojojin Myanmar suka kaddamar da kisan kare-dangi a kan Musulmin yankin.