Gwamnatin Borno ta raba wa masu kanana da matsakaitan sana’o’i tallafin miliyan Naira miliyan 100 a Karamar Hukumar Konduga.
Kaso 70 na wanda aka tallafawar sun fito ne daga Konduga, sai kaso 30 daga Auno, Dalori da Kawuri.
- Mijin Sarauniyar Ingila, Yarima Philip ya rasu
- Sojoji sun kashe mutum 70 a Binuwai
- Yadda sojojin Najeriya suka hallaka ’yan Boko Haram a Gwoza
- Za a dauki Kanawa 4,000 aikin dan sanda
Gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum, wanda ya yi rabon kudin, ya gargadi wadanda aka ba wa da su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.
Ya ce, gwamnatinsa na tallafa wa wadanda rikicin Boko Haram ya ritsa da su ne don farfado da harkar noma a yankunan.
Kazalika, gwamnan ya raba wa hadin gwiwar jami’an tsaron jihar Naira miliyan 5.2 tare da alkawarin gyara musu ababen hawansu da suka lalace.