✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An soma taron jin kai kan Gaza a birnin Paris na kasar Faransa

Faransa ta karbi bakuncin taron jin kai kan Gaza, wanda ba a taba ganin irinsa ba tun bayan harin da Hamas ta kai

Faransa ta karbi bakuncin taron jin kai kan Gaza,wanda ba a taba ganin irinsa ba tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

A wannan taro na Paris da aka shirya a fadar Elysée gwamnatin Isra’ila ba ta aike da wakili ba ,sai dai majiya daga fadar Shugaban na Faransa na cewa shugaba Macron  ya tattauna da Firaminista Benjamin Netanyahu farkon wannan mako.

Bangaren kiwon lafiya a Zirin Gaza na fuskantar gagarumar barazana, a daidai lokacin da alkaluma ke nuna cewa, akwai kimanin mutane dubu 30 da ke fama da mabanbantan raunuka a sanadiyar hare-haren Isra’ila.

Kazzalika Shugaba Macron ya kuma tattauna ta wayar tarho da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sissi da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, wanda kasashensu ke taka muhimmiyar rawa wajen inganta isar da kayan agaji a zirin Gaza, inda Falasdinawa miliyan 2.4 ke fuskantar karancin abinci da ruwan sha.

Rashin kasancewar Isra’ila bai hana hukumar Falasdinu ta aike da Firaministanta  da ya jagoranci tawagar da suka bi ta hanyar mashigin Gaza a wannan lokaci da Masar, wacce ke ikon mashigar Gaza daya tilo da Isra’ila ba shi hannun Isra’ila.

Wani bincike na nuni cewa kungiyoyin agaji na bin diddigin taron, inda suka yi Allah-wadai da rashin samar da kayan agaji, a dai-dai lokaci da Faransa ta sanar da ware kudi milyan 100 na Yuro a matsayin tallafi.

Kungiyoyi masu zaman kansu 13 sun yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa, suna neman “tabbatar da shigar da kayan agaji a Gaza da mutunta dokokin jin kai na kasa da kasa”.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta bukatar agaji ga al’ummar Gaza da gabar yammacin kogin Jordan akan dala biliyan 1.2 har zuwa karshen shekarar 2023.