✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom ya kashe kwamandojin Civilian JTF da dakarunsu a Borno

Duk mutanen da ke cikin motar sintirin jami'an tsaron sun rasu bayan motarsu ta taka bom a Borno

Wasu kwamandoji da jami’an tsaron sa-kai na Civilian JTF sun rasu bayan da suka taka bom da ake zargin na mayakan Boko Haram ne a Jihar Borno.

Dakarun na Civilian JTF sun gamu da ajalinsu a sakamakon taka nakiyar ce a kusa da kauyen Ndufu da ke Karamar Hukumar Ngala a ranar Alhamis.

Wata majiyar tsaro ta shaida mana cewa, “Babban Kwamandan Gambarou, Bukar Goni, da Kwamandan yankin Ngala, Malam Cede were na cikin mutum shida da ke cikin motar kuma dukkansu su n rasu.”

Majiyar ta shaida ce motar sintirin da jami’an tsaron suke ciki ce ta taka bom din da aka binne a gefen hanya, a yayin da suke gudanar da sintiri a Ndufu.

Ta ce jami’an tsaron sun bar garin Ngala da misalinn karfe 3 na rana zuwa Ndufu, inda “kafin su shiga garin Duhu, motarsu ta tarwatse bayan da ta taka bon din, dukkansu suka rasu.”

Wakilinmu ya yi kokain samun karin haske daga ’yan sanda, sai dai ko da ya kira kakakin ’yan sandan Jihar Borno, jami’in bai amsa kiran ba.