An soma ƙidayar ƙuri’u bayan rufe kaɗa ƙuri’a a hukumance a rumfunan zaɓe a birnin Lokoja na Jihar Kogi.
A rumfar zaɓe mai lamba ta 065 da ke yankin Sabon Gari, jami’an Hukumar Zabe ta Kasa INEC sun soma ƙidayar ƙuri’u bayan kammala tantance ƙirga ƙuri’un da aka kaɗa.
- Ya kamata a daidaita lokutan zabe a duk jihohin Najeriya — Goodluck
- Yadda ake sayen kuri’u a Zaben Gwamnan Kogi
Haka ma lamarin yake a rumfar zaɓe mai lamba 067 da ke Otel ɗin Hukumar Yawon Buɗe ta Kogi.
Sai dai kawo yanzu ba a soma ƙidayar ƙuri’un ba a rumfar zaɓe mai lamba ta 012 da ke Kwalejin Crowder a yayin da ma’aikatan zaɓen ke ci gaba da tantance ƙuri’un da aka kada.
Daga nan ne kuma za a ɗauki ƙuri’un da sakamakon da aka samu zuwa mazaɓa, kafin a wuce zuwa ƙaramar hukuma.
‘’Yan takara 18 ne dai suka fafata a zaɓen na yau, sai dai ana ganin takarar ta fi zafi ne tsakanin manyan jam’iyyu uku da suka hada da PDP, APC da kuma SDP.
Aminiya ta ruwaito cewa, a wannan Asabar ce dai ake zaben gwamna a jihohin Imo da Bayelsa da kuma Kogi.
Jihohin sun sauka daga layin lokacin da aka saba gudanar da babban zaɓe ne saboda hukunce-hukuncen kotu da ke ƙwacewa ko kuma su bayar da umarnin a sake zaɓe a jihohin.
Akwai jihohi bakwai da ba su yin zaɓen gwamna tare da saura a sun haɗa da Kogi, da Imo, da Bayelsa, da Edo, da Anambra, da Osun, da kuma Ekiti.