Rundunar Sojin Najeriya ta soma farautar ɓata-garin garin da suka kashe jami’anta 16 da ke aiki da bataliya ta 181 a Karamar Hukumar Bomadi a Jihar Delta.
Daraktan yada labaran rundunar, Tukur Gusau, ya ce gungun wasu matasa ne dauke da muggan makamai suka hallaka dakarun.
Daraktan yada labaran rundunar, Tukur Gusau, ya ce gungun wasu matasa ne dauke da muggan makamai suka hallaka dakarun.
Birgediya-Janar Gusau ya ce daga cikin wadanda ɓata-garin suka kashe, har da kwamandan da ke jagorantar sojojin da wasu masu mukanin Manjo biyu da wani mai mukamin kyaftin ɗaya, sai kuma kananan sojoji 12 da suke aikin wanzar da zaman lafiya a yanki.
A cewarsa, babban hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike tare da kama waɗanda suke da hannu a harin.
Ya ce, “Wasu bata gari a Karamar Hukumar Bomadi a Jihar Delta, sun kai farmaki kan dakarun bataliya ta 181 yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya.
“Sun kashe dakaru 16 kuma wannan abin takaicin ya faru ne a lokacin da sojojin suke kokarin sasanta rikicin kabilanci tsakanin al’ummar Okuoma da Okoloba a Jihar Delta.
“An kai wa tawagar dakarun hari, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar Kwamandan ɗaya, Manjo biyu, Kyaftin ɗaya da sojoji 12.
“Babban Hafsan Sojin Kasa, Janar Christopher Musa ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa domin kama wadanda suke da hannu a harin.
“Kazalika, sojoji ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.
“Ya zuwa yanzu, an kama wasu kuma ana ci gaba da gudanar da bincike don gano makasudin kai a harin.”
Aminiya ta ruwaito, a ranar Alhamis da ta gabata ce wasu ɓata-gari suka kashe sojojin da suka amsa kiran gaggawa domin kai ɗauki kan rikicin ƙabilanci da ya barke tsakanin al’ummar Okuoma da Okoloba a jihar ta Delta.