Ma’aikatar Ayyuka da Muhalli ta Tarayya ta yi kira ga matafiya daga Kudancin Najeriya da ke son zuwa Arewa da su guji bin babbar hanyar Lakwaja zuwa Abuja da ke Jihar Kogi.
Kwanturolan ma’aikatar a Jihar Kogi, Injiniya Jimoh Kajogbola, ne ya yi wannan kira cikin sanarwar da ya fitar a Lakwaja, inda ya bukaci matafiyan da su sake hanya.
- Ana sace gangar danyen 900,000 kullum a Najeriya —Lawan
- CONUA haramtacciyar kungiya ce —Lauyan ASUU
- NAJERIYA A YAU: Yadda Abinci Ke Kashe ’Yan Najeriya
Ya ce, “Sakamakon ambaliyar da aka fuskanta a kasar, Kogin Neja batsewa tare da mamaye babbar hanyar Lakwaja-Abuja a yankin Koton-Karfe, wanda hakan ya sa bin hanyar ya zama abu mai hatsarin gaske.”
Don haka ya shawarci matafiyan da ke son shiga Abuja daga Kudu da su bi hanyar Ilorin-Mokwa-Bida, sannan wadanda suka fito daga Gabas da Kudu maso Kudu, su bi ta hanyyar Makurdi-Lafia.
Ya kara da cewa, daga yanzu har zuwa lokacin da za a samu mafita, matafiya su yi hakuri su ci gaba da bin sauran hanyoyi a madadin wannan.