An shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta hukunta masu hannu a shirya zanga-zangar #EndSARS da ta rikide zuwa tarzoma a Najeriya.
Wani dattijo mazaunin garin Jalingo, Jihar Taraba, James Bulus ya bayar da shawarar a hirar da ya yi da wakilin Aminiya.
- Zanga-zangar EndSARS shiri ne na cin mutuncin Buhari — Rashida Mai Sa’a
- Zanga-zangar #EndSARS ta koma yaki da Musulunci —Abdallah Gadon Kaya
- Ba za mu yafe wa Aisha Yesufu ba —Zahraddeen Sani
- Kasashen waje sun ba mu kudade —Masu Zanga-zangar #EndSARS
Ya yi zargin wadanda suka kitsa rigimar sun yi ne da nufin haddasa yaki da neman jefa gwamnati mai ci a cikin tsaka mai wuya.
Dattijon ya ce ya zama jazaman gwamnati ta gano masu hannu a cikin shirin wanda ya ce cin amanar kasa ne.
Ya bayyana mamakinsa kan yadda jami’an tsaro suka kasa bankadowa da kuma dakile zanga-zangar wadda ta koma abin da ya kira fasadi.
A cewarsa, da zarar wadanda suka hura wutar rigimar sun cimma burinsu, za su arce zuwa kasashen waje inda suke da kadarori su bar ‘yan Najeriya cikin tashin hankali.
Ya kuma bukaci gwamnati da kada ta saurari kasashen waje wadanda da ya ce a kullum burinsu shi ne su ga kasar ta wargaje.
Mista James ya ce ya zama tilas Shugaba Buhari ya dauki matakan nurkushe masu neman jefa kasar cikin yaki da sunan zanga-zangar lumana.
Kasashen, a cewarsa, ba da gaske suke yi da cewa a bai wa jama’a ’yancin zanga-zangar lumana ba domin kowa ya ga yadda Amurka da Faransa suka murkushe makamanciyarta a kasashensu.
Ya jaddada cewa muddin shugaba Buhari bai dauki mataki cikin gaggawa ba to za a yi wa kasar sakiyar da ba ruwa.
Ya kuma nemi ’yan kasa na gari su bai wa gwamnati hadin kai domin samun nasaran magance wanna mumnunar lamari.