Wani dattijo mai shekara 60 a duniya ya rasu a wani sabon hatsarin kwalekwale a Jihar Sakkwato.
Hatsarin kwalekwalen y aritsa sa Dattijon da da abokan tafiyarsa 34 ne a yankin Tangwale da ke Shiyyar Ɗubɗaye a ranar Asabar.
Mashawarcin Shugaban Jihar Sakkwato kan Agajin Gaggawa, Nasiru Garba Kalambaina, ya tabbatar wa Aminiya cewa masu aikin ceto sun yi nasarar ceto ragowar fasinjojin kwalekwalen 34 da ranau, bayan hatsarin.
“Wani dattijo dan shekara 60 dan asalin ƙauyen Tangwale ya rasu amma an gano gawarsa an yi mata jana’iza yadda Musulunci ya tanadar,” in ji Kalambaina.
Mashawarcin gwamnan ya jagoranci wasu jami’an gwamnati da Hukumar Agajin Gaggawa ya kasa (NEMA) zuwa ƙauyen, domin gaisuwar ta’aziyya.