Hukumar Kwallon Kafar Turai UEFA, ta mayar da wasan karshe na gasar cin Kofin Zakarun Turai da za a fafata tsakanin Chelsea da Manchester City zuwa kasar Portugal.
Wasan da za a fafata ranar 29 ga watan Mayun, an mayar da shi birnin Porto na kasar Portugal daga kasar Turkiyya sakamakon kullen annobar Coronavirus.
- Wajibi ne mu taimaka wa gwamnati wajen samar da tsaro — Sarkin Jema’a
- Sarkin Zazzau da Hakimai 76 sun yi Hawan Sallah
Kazalika, sauyin na zuwa ne a sakamakon kasancewar Turkiyya na daga cikin kasashen da Birtaniya ta dakatar da ’yan kasarta daga zuwa.
Portugal na da daga cikin kasashen da Gwamnatin Birtaniya ta kyale ’yan kasarta su je don haka ’yan kwallo da magoya bayansu na halartar wasan.
An ruwaito shugaban UEFA, Aleksander Cefarin yana cewa, “Ba za mu hana magoya baya zuwa kallo kafada-da-kafada ba kuma ina farin ciki da aka samu matsaya.”
Rahotanni sun bayyana cewa, an kayyade wa kowace kungiyar gabatar da ’yan kallo dubu shida-shida da za su halarci wasan a filin wasan FC Porto mai daukar mutum 50,033.
An ruwaito shugaban UEFA, Aleksander Ceferin yana cewa, “Ba za mu hana magoya baya zuwa kallo kafada-da-kafada ba kuma ina farin ciki da aka samu matsaya.”
UEFA da Gwamnatin Birtaniya da Hukumar Kwallon Kafar Birtaniya sun tattauna kan yiwuwar yin wasan a filin wasa na Wembley sai dai an gaza cimma matsaya kan batun killace manyan mutane da masu daukar nauyin gasar da ’yan jarida.